Jam’iyyar PDP tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike, ta tabbatar da tsohon ɗan majalisar tarayya, Sandy Onor, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.


Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar, Samuel Ortom, ne ya sanar da hakan a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.


Ortom, wanda tsohon gwamnan jihar Benue ne, ya ce Onor ya zama ɗan takarar jam’iyyar ne ta hanyar yarjejeniya bayan tattaunawa da wakilan jihohi 36 da kuma Abuja.


Shi ma shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Abdullahi Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyar na da ɗan takara guda ɗaya kacal, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa PDP za ta taka muhimmiyar rawa a zaɓen 2027.


A jawabinsa na karɓar takarar, Sandy Onor ya yi alƙawarin gudanar da yakin neman zaɓensa da jajircewa.