Jirgin farko da ke ɗauke da ‘yan Ghana da aka kwashe daga Afirka ta Kudu saboda tashin hankalin da ya shafi adawa da baƙin haure ya isa birnin Accra ranar Laraba, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ta bayyana.

Ana sa ran kusan ‘yan Ghana 800 ne za su bar Afirka ta Kudu, bayan gwamnatin Ghana ta shirya jiragen dawo da su sakamakon zanga-zangar ƙin jinin baƙi da ta ɓarke a wasu sassan ƙasar.

Wani mai ɗaukar hoto na AFP ya ga daruruwan ‘yan Ghana suna tsaye a layi a Filin Jiragen Sama na O.R. Tambo da ke wajen Johannesburg da safiyar Laraba domin komawa gida.

Shafin FlightAware da ke bibiyar zirga-zirgar jiragen sama ya nuna cewa jirgin ya tashi ne bayan ƙarfe 11:00 na safe agogon Afirka ta Kudu.

Ofishin Jakadancin Ghana da ke Afirka ta Kudu ya ce ana sa ran kusan mutane 300 ne suka kasance cikin jirgin farko da ya isa Accra ranar Laraba.

Gwamnatin Ghana ta kuma yi alƙawarin bai wa waɗanda aka dawo da su tallafin kuɗi domin sake farfaɗo da rayuwarsu tare da ba su kulawar lafiyar ƙwaƙwalwa da zamantakewa.

Afirka ta Kudu dai na fama da matsanancin rashin aikin yi da ya haura kashi 30 cikin ɗari, lamarin da ya janyo yawaitar zanga-zangar adawa da baƙin haure a lokuta daban-daban, ciki har da a ‘yan makonnin nan.

Sai dai gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi kira ga ‘yan ƙasar da su kwantar da hankalinsu tare da rungumar baƙin hauren da ke zaune cikin ƙasar bisa doka.