Isra’ila ta kai hari a birnin Beirut, babban birnin Lebanon, karo na biyu tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a watan da ya gabata.
Dakarun Isra’ila (IDF) sun ce an shirya harin ne kan wani takamaiman buri, sai dai ba su bayar da cikakken bayani ba.
Kafofin yaɗa labarai na Isra’ila sun ambato wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba suna cewa wanda aka nufa da harin wani jagoran ƙungiyar masu ɗauke da makamai masu samun goyon bayan Iran ne.
Rahotanni sun ce Isra’ila ta sassauta harin kan Beirut ne bisa roƙon Shugaban Amurka, Donald Trump, yayin da hare-haren suka biyo bayan jerin farmakin da Isra’ila ta kai kan gine-ginen Hezbollah a kudancin Lebanon, kamar yadda IDF ta bayyana.
Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran dai na ci gaba da zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar.
An ga baƙin hayaƙi na tashi tsakanin gine-gine a yankin Dahieh, wanda ake ganin cibiyar Hezbollah ce a Beirut, bayan hare-haren baya-bayan nan da Isra’ila ta kai.
Haka kuma an ji mazauna yankin suna kiran maƙwabta da ƴan uwansu yayin da jami’an agaji ke ƙoƙarin kai ɗauki ga waɗanda lamarin ya shafa.