Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana damuwarta kan ci gaba da tabarbarewar matsalar tsaro da kuma ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar.

A cikin saƙon barka da Sallah da Shugaban NLC, Joe Ajaero ya fitar, ƙungiyar ta ce ma’aikatan Najeriya da talakawa na cikin matsanancin ƙunci sakamakon wasu manufofi da ake aiwatarwa.

Ya ce miliyoyin ‘yan ƙasa na fuskantar tsadar rayuwa da ke ƙara jefa su cikin talauci, tare da yin kira ga ‘yan siyasa da su sake duba tasirin matakan tattalin arzikinsu.

NLC ta kuma bukaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar.

Haka kuma Ajaero ya jaddada bukatar gwamnatoci su mayar da hankali wajen kare rayukan ‘yan ƙasa tare da samar da muhimman abubuwa kamar abinci, kiwon lafiya, ilimi da kuma damar samun aikin yi.