Wani rahoto da ake danganta shi da Amurka ya yi zargin cewa wasu Fulani masu ɗauke da makamai na ci gaba da mamaye gonakin Kiristoci tare da kai hare-hare kan wuraren ibada na Kiristoci da Musulmai a Najeriya.

Rahoton ya bayyana cewa a ‘yan shekarun nan, wasu masu ɗauke da makamai da ake dangantawa da Fulani sun kai hare-hare a kan al’ummomi daban-daban, ba wai Kiristoci kaɗai ba, a sassa daban-daban na ƙasar.

Haka kuma ya yi iƙirarin cewa wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi na Fulani ‘yan bindiga suna kai hare-hare kai tsaye, yayin da wasu lokuta kuma suke haɗa kai da ‘yan fashin daji da kuma wasu ƙungiyoyin ta’addanci, da nufin yaɗa wani tsarin ra’ayin addini mai tayar da hankali.

Rahoton ya kuma ce yankin Arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar rikice-rikice masu alaƙa da ƙabilanci da addini.

A baya-bayan nan kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana tauye wa Kiristoci ‘yancinsu a Najeriya, zargin da gwamnatin ƙasar ta musanta.