Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a ranar Laraba, ya kai ziyara ga abokin karawarsa, tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a Abuja.

A yayin sanar da sakamakon zaɓen, shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, David Mark, ya bayyana cewa Atiku ne ya yi nasara da ƙuri’u 1,846,370, inda ya kayar da Amaechi da kuma Mohammed Hayatu-Deen wanda ya zo na uku.

Bayan sanar da sakamakon, an fara samun raɗe-raɗi kan yiwuwar rikici, ganin cewa tun kafin kammala kirga ƙuri’u wasu ‘yan takara sun nuna rashin gamsuwa da tsarin zaɓen.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce ya kai wa Amaechi ziyara a gidansa da ke Abuja, inda suka tattauna kan halin da ƙasar ke ciki, musamman matsin tattalin arziki, rashin tsaro da kuma buƙatar gaggauta ceto Najeriya daga matsalolinta.

Ziyarar ta jawo fassara daban-daban a fagen siyasa, inda wasu ke ganin hakan na nuni da ƙoƙarin sulhu tsakanin manyan ‘yan adawa, yayin da ake shirin babban zaɓen 2027.

Shi ma Mohammed Hayatu-Deen ya nuna damuwa kan yadda aka gudanar da zaɓen fitar da gwani, lamarin da ya ƙara tayar da ƙura a cikin jam’iyyar ADC.

Masana siyasa kuma na ganin cewa irin wannan rikici bayan zaɓen fitar da gwani na iya haddasa rabuwar kai a tsakanin ‘yan takara idan ba a shawo kansa cikin lokaci ba.