Amurka na ƙara matsa wa Iran lamba ta hanyar sabbin matakan takunkumin tattalin arziƙi, da nufin tilasta mata buɗe Mashigar Hormuz.
Sakataren Kuɗin Amurka, Scott Bessent, ya bayyana cewa Amurka za ta hana jiragen sama mallakin kamfanonin Iran sauka a wasu filayen jiragen sama, a wani mataki da ake ganin zai ƙara matsin tattalin arziƙi kan ƙasar.
Wannan sanarwa ta biyo bayan matakan da Ma’aikatar Kuɗin Amurka ta ɗauka kwana ɗaya kafin hakan, inda ta bayyana sabbin tsare-tsare da suka shafi wata hukuma da ke karɓar haraji kan jiragen ruwan da ke wucewa ta Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanya ta jigilar man fetur a duniya.
Matakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin diflomasiyya tsakanin Washington da Tehran ke ci gaba da ƙamari, yayin da Amurka ke neman ƙara matsin lamba kan Iran ta fuskar tattalin arziƙi da kasuwanci.