Hisbah a ƙaramar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina ta kama wani mutum bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekara 11 fyaɗe a unguwar Bakin Sabuwar Kasuwa.

A cewar sanarwar da jami’in sashen fasahar sadarwa na Hisbah a Dutsinma, Malam BYAREEMA ya fitar, mazauna unguwar ne suka kama wanda ake zargin tare da tsare shi kafin jami’an Hisbah suka isa wurin domin karɓarsa da fara bincike.

Sanarwar ta ƙara da cewa an samu wanda ake zargin cikin maye yana riƙe da wandonsa a hannu.

Hukumar Hisbah ta yaba da haɗin kan al’umma wajen taimakawa jami’an tsaro, tare da kira ga iyaye su ƙara sanya ido kan yaransu musamman yayin bukukuwan Babbar Sallah.

Hukumar ta ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.