Gwamnatin ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja ta umarci mazauna yankunan da ambaliya ta shafa a bara da su fice daga wuraren saboda barazanar sake aukuwar ambaliya.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran shugaban ƙaramar hukumar, Haruna Saidu Kinbokun ya fitar ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu taruwar ruwa a yankin sakamakon toshewar hanyar ruwa da ake zargin aikin sake gina layin dogo ya haddasa.
Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa aikin da kamfanin CPN ke yi ya kawo cikas ga hanyar ruwa na ɗan lokaci, lamarin da ya janyo kwararar ruwa mai yawa da ka iya haifar da sabon ambaliya.
Shugaban ƙaramar hukumar Mokwa, Hon. Jibrin Abdullahi Muregi, ya umarci kamfanin da ya gaggauta buɗe hanyar ruwa domin hana sake afkuwar irin wannan iftila’i.
Haka kuma, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Dr. Hussaini Ibrahim domin duba halin da ake ciki tare da bayar da shawarwari kan hanyoyin da za su dakile sake aukuwar ambaliya a nan gaba.