Siyasar Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ana kallonta a matsayin siyasa mai cike da ƙalubale da ke yawan bai wa gwamnoni kunya, inda ake ganin tsarin “siyasar ubangida” na da tasiri wajen sauya akalar abubuwa ba tare da hasashe ba.
A irin wannan yanayi, ana zargin cewa tsarin siyasar jihar ba ya barin ‘yan takara su tabbatar da makomarsu cikin sauƙi, lamarin da ya sa a wannan karo manyan ‘yan takarar gwamnan jihar suka kadu da sakamakon zaɓen fidda gwani da aka gudanar.
Daga cikin masu neman tikitin takarar akwai Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, Sanata mai ci Umaru Shehu Buba, da kuma Nuru Mani Soro, jagoran yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu a Bauchi a 2023, sai kuma Bala Mai Jama’a Wunti, tsohon shugaban kamfanin NNPC.
Sai dai a ƙarshe, tsohon gwamnan jihar tsakanin 2015 zuwa 2019, Barista Muhammed Abdullahi Abubakar, ne ya samu tikitin takara, duk da cewa ya taɓa fuskantar rashin nasara a baya, yanzu kuma zai yi ƙoƙarin kammala wa’adin da ya rage masa.
Wannan mataki ya haifar da rashin jin daɗi a wajen wasu daga cikin abokan hamayyarsa. Yusuf Maitama Tuggar ya bayyana ra’ayinsa a wata hira da BBC cewa bai gamsu da tsarin ba, yana mai cewa da a bar zaɓi na gaskiya ya gudana da wanda ya ci ya ci, wanda ya fadi kuma ya fadi.
Ya kuma ce an sanar da su ne daga shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa cewa an zaɓi M.A. Abubakar a matsayin ɗan takara, abin da ya ce bai yi masa daɗi ba, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin adalci.