Hukumomi a Kenya sun kama ɗalibai takwas bisa zargin suna da hannu a mummunar gobarar da ta tashi a wata makarantar kwana ta ƴanmata da ke Gilgil, wadda ta yi sanadin mutuwar ɗalibai 16.
Sashen binciken manyan laifuka na ƙasar ya tabbatar da kamen, yana mai cewa binciken farko-farko ya nuna akwai alamun cewa an tayar da gobarar da gangan.
Gobarar ta tashi ne a ɗakin kwanan ɗalibai inda ta lalata wani sashe na ginin mai hawa biyu.
Hukumomi sun ce ƙwararrun masu bincike na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an bincike sun riga sun tattauna da ɗalibai, malamai da wasu shaidu, tare da nazarin faifan bidiyon kyamarorin tsaro domin gano yadda gobarar ta fara.