Yarima Saud bin Mishal bin Abdulaziz, mataimakin gwamnan yankin Makkah kuma mataimakin shugaban Kwamitin Dindindin na Hajj da Umrah, ya bayyana cewa kakar Hajjin 2026/1447 AH ta kasance mai nasara, sakamakon ingantaccen tsarin tsaro, tsari da ayyuka masu haɗaka da suka bai wa mahajjata damar gudanar da ibadarsu cikin natsuwa da aminci.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa ta talabijin a daren kammala aikin Hajjin bana, inda ya ce Saudiyya ta kammala kakar Hajji cikin nasara, tare da tabbatar da sauƙi da kwanciyar hankali ga mahajjata a duk matakan ibada.
Yarima Saud ya ƙara da cewa wannan nasara ta nuna cewa Hajji ba kawai ibada ba ce ta shekara-shekara, amma wata dama ce ta sabunta alƙawarin Saudiyya na ci gaba da hidima ga Musulunci da Musulmai.
A baya, Hukumar Kasa ta Kididdiga ta Saudiyya ta bayyana cewa jimillar mahajjata a wannan shekara ta kai 1,707,301, inda 1,546,655 suka fito daga ƙasashe 165, yayin da 160,646 kuma mazauna Saudiyya ne.
Adadin ya zarce na shekarar da ta gabata, sai dai har yanzu bai kai na shekarar 2024 ba da aka samu sama da mahajjata miliyan 1.83. Ana sa ran kammala aikin Hajjin a hukumance ranar Asabar.
Ayyukan Hajji na bana sun fara ne da isowar mahajjata Mina, inda aka gudanar da tsauraran matakan tsaro da shirye-shiryen hidima domin sauƙaƙa gudanar da ibada. A cikin kwanaki shida na Hajji, mahajjata sun yi tsayuwar Arafat, sun kwana a Muzdalifah, sun yi jifar shaiɗan, tare da kammala da ɗawafin bankwana a Masallacin Ka’aba.