Matakin ya biyo bayan yawaitar masu daukaka ko shuhura wato influencers dake bayyan dukuyar da suka mallaka a kafafen sada zumunta.


Ƙasar na sa ido kan accounts da ke baje kolin motocin alfarma da manyan gidaje da tufafin masu tsada da kayan ado na zinariya da lu’ulu’u da jiragen sama masu zaman kansu, da kuma rayuwar da ta ta’allaka kan bautar kuɗi.


Daga cikin shahararrun influencers da wannan mataki ya shafa ita ce Wang Hongquanxing, wadda aka fi sani a intanet da suna “Kim Kardashian ta China.”


Tana da miliyoyin mabiya, kuma ta shahara ne saboda nuna tufafin alfarma da kayan ado masu tsada da tafiye-tafiye da rayuwar attajirai.


A cewar Gwamnatin Kasar China manufar wannan mataki shi ne, samar da ingantacciyar al’adar amfani da intanet da kuma hana yaɗa son zuciya da bautar abin duniya.