Kungiyar kare hakkin dan adama ta Amnesty International, ta horas da matasa 30 a jihar Cross River kan hanyoyin kare hakkokin dan Adam da kuma yadda za su gano tare da bayar da rahoton take hakki a cikin al'ummar su.
An gudanar da horaswar ne na tsawon kwanaki biyu karkashin wani shiri wanda Asusun Ofishin Jakadancin Jamus ya dauki nauyin tallafawa.
Shirin na da nufin samar da sabbin masu fafutukar kare hakkokin dan adama da za su iya tattara bayanai kan take hakki, neman tabbatar da adalci ga wadanda aka zalunta tare da hada kai da hukumomi domin magance matsalolin da ke addabar al'umma.
Da take jawabi a yayin taron da aka gudanar a Calabar, Manajar Shirye-shiryen Amnesty International, Barbara Magaji, ta ce an koyar da mahalarta dabarun gano take hakkoki, tattara hujjoji da kuma yadda za su mayar da martani cikin kwarewa da bin ka'idojin kare hakkin dan adama.