Wani ɓangare na jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya bayyana dalilan da suka sa ya ayyana tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takararsa na shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce Jonathan ne ya fi cancanta ya jagoranci Najeriya a wannan lokaci, tana mai nuni da nasarorin da aka samu a lokacin mulkinsa, da jajircewarsa wajen kare dimokuraɗiyya da kuma yadda ya gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali.

Da yake jawabi bayan wani taron masu ruwa da tsaki, shugabannin ɓangaren sun bayyana cewa mulkin Jonathan ya kasance lokaci na ci gaban tattalin arziki, haɗin kan ƙasa da kuma girmama cibiyoyin dimokuraɗiyya.

Sun ce a lokacin gwamnatinsa an samu bunƙasar tattalin arziki, ƙaruwa a zuba jarin ƙasashen waje, inganta ababen more rayuwa da kuma sauye-sauye a fannoni kamar noma, ilimi da sadarwa.

Mashawarci ga Tanimu Turaki, Ibrahim Abdullahi, ya ce halin ƙuncin rayuwa da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a yau sun sa mutane da dama suna sake tuna irin yanayin da ƙasar ta kasance a lokacin gwamnatin Jonathan.

Ya kuma yabawa tsohon shugaban ƙasar kan yadda ya amince da sakamakon zaɓen 2015, yana mai cewa hakan na daga cikin manyan misalan sadaukarwa da kishin dimokuraɗiyya a tarihin Afirka.

“A lokacin da ƙasar ke cikin wani yanayi mai muhimmanci, Jonathan ya fifita zaman lafiya da haɗin kan ƙasa a kan muradinsa na siyasa. Wannan mataki ya ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya tare da ƙara masa kima a idon duniya,” in ji Abdullahi.

Jam’iyyar ta ce mika mulki cikin lumana da Jonathan ya yi ya taimaka wajen kauce wa rikice-rikice tare da kafa kyakkyawan tarihi ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

Sai dai ɓangaren ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin nasarorin da aka samu a lokacin gwamnatocin PDP sun lalace, yana mai danganta hakan da matsalolin tattalin arziki, tsadar rayuwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma matsalolin tsaro da ake fuskanta a halin yanzu.

A cewarsu, gogewa, tawali’u da biyayya ga manufofin dimokuraɗiyya su ne manyan dalilan da suka sa suka zaɓi Jonathan a matsayin ɗan takararsu.

“Ba saboda ya taɓa zama shugaban ƙasa ba ne muka zaɓe shi, sai dai saboda tarihin ayyukansa da irin shugabancin da ya nuna. Mun yi imanin cewa Najeriya na buƙatar irin wannan shugabanci a wannan lokaci,” in ji Ibrahim Abdullahi.

A ƙarshe, ɓangaren Turaki na PDP ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da sauran ’yan Najeriya da su mara wa wannan kuduri baya domin samar da abin da ya bayyana a matsayin shugabanci mai haɗa kan ƙasa, farfaɗo da tattalin arziki da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya.