Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ƙarƙashin jagorancin Sanata Seriake Dickson ta ayyana tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.
An sanar da Obi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ne a yayin babban taron NDC da aka gudanar a Abuja ranar Asabar.
Bayan karɓar tutar jam’iyyar, Obi ya bayyana tsohon gwamnan Jihar Kano, Musa Kwankwaso, a matsayin abokin takararsa.
Fitowar Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC ya sake ƙara zafi a fafatawar siyasar 2027 tsakanin manyan 'yan takara daga manyan jam’iyyun ƙasar.

Matakin na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC.
Tun da farko dai Atiku da Obi sun haɗu da ADC tare da wasu fitattun 'yan adawa a watan Yulin 2025, a wani yunƙuri na samar da haɗin kan adawa domin ƙalubalantar APC a zaɓen 2027. Sai dai daga bisani Obi da Kwankwaso sun fice daga jam’iyyar tare da komawa NDC.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa shigowar Obi da Kwankwaso cikin NDC, tare da magoya bayansu na ƙungiyoyin Obidient Movement da Kwankwasiyya Movement, zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi da tasiri a fagen siyasar Najeriya gabanin babban zaɓen shekarar 2027.