Gwamnatin Jihar Kano ta fara shirin mayar da dutsen Dala da Goron Dutse cibiyoyin binciken tarihi da yawon bude ido domin bunkasa harkokin tarihi da al’adun gargajiya a jihar.

Shugaban Hukumar Tarihi da Al’adu ta Jihar Kano, Arc. Ahmad Abba Yusuf ne ya bayyana hakan a sakonsa na cikar Gwamna Abba Kabir Yusuf shekaru uku a mulki.

Ya bayyana cewa shirin na daga cikin matakan da hukumar ke dauka na alkintawa da bunkasa wuraren tarihi masu muhimmanci a Kano tare da kara haɓaka harkokin yawon bude ido.

Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa an gyara wuraren tarihi yayin da ake ci gaba da aikin sake gina wasu, sannan an fara kokarin farfado da bikin baje kolin al’adu na KANFEST domin bunkasa al’adu da yawon bude ido a jihar.

Ya kara da cewa hukumar na aiwatar da tsare-tsare na kare Ganuwar Kano da kofofinta tare da samar da shagunan sana’o’in gargajiya da kuma gidan cin abincin Hausawa domin tallafawa masu sana’o’in gargajiya da bunkasa tattalin arziki