Kungiyar Masu Kananan sana’oi ta Najeriya (ASBON) ta bayyana cewa kimanin kananan da matsakaitan sana’o’i miliyan biyu ne suka rufe harkokinsu cikin shekaru uku na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, duk da alkawarin tallafin naira biliyan 200 da gwamnatin tarayya ta yi domin rage radadin sauye-sauyen tattalin arziki.

‎Kungiyar ta danganta rugujewar kasuwancin da cire tallafin man fetur, sauye-sauyen tsarin canjin kudaden kasashen waje, tashin farashin kayayyaki, karuwar kudin gudanar da kasuwanci da kuma raguwar karfin sayen jama’a.

‎A watan Yulin 2023, Shugaba Tinubu ya sanar da wani shirin tallafi na naira biliyan 75 ga masana’antu da kuma naira biliyan 125 ga kananan da matsakaitan sana’o’i domin taimaka musu su jure kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

‎Shugaban kungiyar na kasa, Dakta Femi Egbesola, ya ce wasu daga cikin mambobinsu sun samu tallafin naira dubu 50 da aka ware wa kananan sana’o’i, amma adadin kudin bai wadatar wajen magance matsalolin da ‘yan kasuwa ke fuskanta a halin yanzu ba.