Babban mai jagorantar tattaunawar Iran, Mohammad Ghalibaf, ya bayyana cewa kasarsa ba za ta amince da wata yarjejeniya da Amurka ba matukar ba ta tabbatar da kare hakkin al’ummar Iran ba.
A wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na gwamnatin Iran ranar Lahadi, Ghalibaf ya ce gwamnati ba za ta sanya hannu kan wata yarjejeniya ba har sai ta gamsu cewa an mutunta da kuma kare muradun ‘yan Iran.
Ya kara da cewa masu tattaunawar Iran ba sa yarda da kalamai ko alkawurran bangaren da suke tattaunawa da shi, yana mai jaddada cewa za su tsaya tsayin daka wajen kare bukatun kasarsu.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da Iran da Amurka ke ci gaba da musayar shawarwari da tsare-tsaren da za su iya zama tubalin wata yarjejeniya domin kawo karshen yakin da ya barke a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya shafi yankuna da dama na Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na Amurka sun nuna cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya aika wa Tehran da wani sabon tsarin yarjejeniya domin Iran ta yi nazari a kai, wanda aka ce ya kunshi wasu sharudda masu tsauri fiye da na baya.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayanin sabbin sharuddan ba.
Iran na ganin cewa daga cikin muhimman hakkokinta akwai dage takunkumin tattalin arziki da aka kakaba mata, da kuma sakin kadarorinta da aka daskarar a bankunan kasashen waje.
Haka kuma, gwamnatin Iran na kallon ikon sa ido da kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz a matsayin wani bangare na hakkokinta na kasa.
Mashigin Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin safarar makamashi a duniya, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen zirga-zirgar danyen mai da iskar gas zuwa kasuwannin duniya.
Iran ta bayyana cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma dole ne ta kare muradun kasarta da kuma tabbatar da hakkokin al’ummarta.