Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar masu gadin dazuka 1,000 a jihar Oyo domin karfafa tsaro da yaki da masu garkuwa da mutane.

Haka kuma, shugaban kasar ya bayar da umarnin tura rundunar tsaro ta musamman mai kwarewa wajen gudanar da ayyukan ceto domin kara kaimi wajen kubutar da dalibai da malamai da aka sace daga makarantu uku a karamar hukumar Oriire.

Wannan na zuwa ne yayin da Kungiyar Malaman Najeriya (NUT) ta ayyana yajin aiki na sai baba-ta-gani ga dukkan malamai a makarantun firamare da sakandare na jihar Oyo, tare da sanar da shirinta na gudanar da gangamin nuna goyon baya a fadin kasar domin matsa wa gwamnati lamba ta kubutar da wadanda aka sace.

Tinubu ya tura manyan jami’an tsaro

A wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce wata babbar tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyara garuruwan Esiele da Yawota domin isar da sakon shugaban kasa ga al’umma.

Tawagar ta hada da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Tunji Disu.

Gbajabiamila ya ce Shugaba Tinubu na matukar damuwa da lamarin kuma ya bayar da dukkan umarnin da suka dace domin tabbatar da ceto daliban da malamai cikin koshin lafiya.

Ya kuma tabbatar wa iyaye da mazauna yankin cewa aikin ceto zai kasance cikin hikima da tsari, tare da amfani da hanyoyin tsaro da tattaunawa domin kare rayukan wadanda aka sace.

Za a dauki masu gadin dazuka 1,000

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a dauki masu gadin dazuka 1,000 tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Oyo domin sanya ido da dakile ayyukan ‘yan ta’adda a yankunan dazuka.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya ce shugaban kasa ya amince da daukar wadannan jami'ai cikin gaggawa, yayin da sauran bukatun tsaro da al'ummar yankin suka gabatar za a yi nazari a kansu.

NUT ta ayyana yajin aiki

A wani bangare kuma, kungiyar NUT ta umurci dukkan malamai a makarantun gwamnati na firamare da sakandare a jihar Oyo da su dakatar da aiki daga ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026.

Shugaban kungiyar na kasa, Audu Amba, da Sakatare Janar, Dr. Clinton Ikpitibo, sun bayyana cewa kungiyar ta dauki matakin ne saboda ci gaba da tsare dalibai da malamai ba tare da an samu nasarar kubutar da su ba.

Kungiyar ta ce halin da wadanda aka sace ke ciki abin tausayi ne kuma ya jefa iyalansu da daukacin bangaren ilimi cikin damuwa.

NUT ta kuma umarci rassanta a dukkan jihohin Najeriya da su gudanar da gangamin nuna goyon baya a ranar 2 ga Yuni domin kira ga gwamnati ta dauki matakan gaggawa wajen kubutar da wadanda aka sace da kuma inganta tsaron makarantu.

Ribadu: Ba za mu yi kasa a gwiwa ba

Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kawo karshen wannan mummunan aiki.

Ya ce sace yara kanana har da jarirai masu shekaru biyu babban abin takaici ne, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin dawo da zaman lafiya.

SERAP ta nemi shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya

Kungiyar SERAP ta bukaci Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, da ya dauki mataki kan matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a Najeriya.

Kungiyar ta ce yawaitar sace-sace, kashe-kashe da korar jama'a daga gidajensu a jihohi da dama na bukatar kulawar gaggawa daga kasashen duniya.

Baptist Convention ta nuna damuwa

Kungiyar Baptist ta Najeriya ta bayyana matukar damuwa kan sace dalibai da malamai, musamman ganin cewa akwai karamin yaro mai shekaru biyu cikin wadanda aka sace.

Shugaban kungiyar, Rev. Israel Akanji, ya ce abin takaici ne yadda yara da malamai ke ci gaba da kasancewa cikin daji suna fuskantar ruwan sama da mawuyacin hali ba tare da kariya ba.

Ya bukaci gwamnati, sarakuna, shugabannin al’umma da kungiyoyin farar hula da su hada hannu wajen yaki da matsalar rashin tsaro, tare da sake kira da a kafa ‘yan sandan jihohi domin inganta tsaro a fadin kasar.

Makinde ya bukaci hadin kai

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya roki jama’a da kada su mayar da lamarin siyasa ko su rika dora laifi kan gwamnatin tarayya ko ta jiha.

Ya ce lokaci ne na hada kai domin kubutar da dalibai da malamai, yana mai tabbatar wa iyalan wadanda aka sace cewa gwamnati na aiki dare da rana tare da jami’an tsaro domin ganin sun dawo gida lafiya.