Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta sanar da kafa wani sashe na musamman da zai mayar da hankali wajen inganta lafiya da walwalar mata musamnan‘yan mata, tare da ba da fifiko kan abunda ya shafi jinin al'ada da abunda ke tattare da shi.
Wakilinnmu Adamu Abdullahi ya rawaito mana cewa, Kwamishinan Lafiya na Jihar Dakta Abubakar Labaran Yusuf, shi ne ya bayyana hakan a wata zantawa da manema labarai a yayin bikin Ranar Tsaftar Jinin Al'ada ta Duniya, wadda ake gudanarwa a kowace ranar 28 ga watan Mayu na kowacce Shekara.
Dakta Yusuf ya bayyana cewa an ware wannan rana ne domin wayar da kan mata da ‘yan mata kan hanyoyin da suka dace na kula da tsaftar jikinsu yayin jinin al'ada
Ya jaddada cewa Gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da jajircewa wajen inganta lafiyar mata da yara a faɗin jihar.
Ya kuma ƙara da cewa, ‘yan mata da dama na fuskantar ƙyama, tsoro da damuwa ta fuskar tunani a lokacin al’adarsu.
Ya ce ma’aikatar na aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyoyi masu zaman kansu, hukumomin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki domin wayar da kan ‘yan mata kan hanyoyin da suka dace da lafiya wajen kula da jiki a irin wannan lakoci.
Majalisar Ɗinkin Duniya ce dai ta ayyana Ranar Tsaftar Jinin Haila ( al'ada) ta Duniya, kuma ana gudanar da ita a kowace shekara, kuma Taken bikin bana shi ne “muyi aiki Tare Domin Samar da Duniya Mai Sauƙin Kula da Jinin Haila ( al'ada)