Rundunar Ƴansandan Najeriya reshen Jihar Yobe ta sanar da gano wani haramtaccen wurin ƙera makamai a garin Potiskum, tare da kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a aikin.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana wannan nasara a matsayin ɗaya daga cikin manyan ci gaban da ta samu wajen yaƙi da laifuffuka a jihar.

Kakakin rundunar a jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce kamen ya biyo bayan sabbin tsare-tsaren da Kwamishinan ƴansandan jihar ya ƙaddamar domin daƙile ayyukan ta’addanci da sauran laifuffuka a faɗin Yobe.

A cewarsa, a ranar 2 ga Yunin 2026 da misalin ƙarfe shida na yamma, rundunar ta samu sahihan bayanan sirri cewa wasu maƙera na ƙera bindigogin katako da sauran makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Bayan samun bayanan ne rundunar yankin Potiskum tare da haɗin gwiwar hedikwatar ƴansanda suka gudanar da samame a wani wurin maƙera da ke Tasha Adua kan titin Danchuwa a Potiskum.

SP Abdulkarim ya ce a yayin samamen an kama mutane bakwai, tare da ƙwace wasu kayayyaki da suka haɗa da bindigogi da aka ƙera da sauran abubuwa.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan waɗanda ake zargin domin gano abokan hulɗarsu, masu sayen makaman da kuma manufar amfani da su.