Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana goyon bayanta ga yajin aikin gama gari da Kungiyar Malaman Najeriya (NUT) ta fara a fadin kasar, tare da yin kira da a gaggauta sakin dalibai da malamai da masu garkuwa da mutane suka sace a sassa daban-daban na kasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, wadda Shugabanta, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu, NLC ta bayyana cewa yajin aikin ya zama wajibi saboda tabarbarewar matsalar tsaro da ke addabar malamai da daliban makarantu a kasar nan.
Kungiyar ta ce matakin da malaman suka dauka na nuna kudirinsu na kare rayukansu yayin da hare-hare kan cibiyoyin ilimi da ma’aikatan ilimi ke ci gaba da karuwa.
Sanarwar ta ce: “Wannan mataki na kasa baki daya da aka tsara cikin tsari yana nuna aniyar malamai ta daukar makomarsu a hannunsu maimakon su ci gaba da jira har sai an kashe su baki daya.”
NLC ta kuma bayyana cewa yajin aikin ya kamata ya zama wata babbar tunatarwa ga gwamnatoci a dukkan matakai da su dauki matakin gaggawa wajen magance matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a fadin Najeriya.
Sanarwar ta kara da cewa: “Wannan mataki kuma wata hanya ce ta tunatar da gwamnatoci cikin lumana amma ba za a iya yin watsi da ita ba, cewa su dauki matsalar rashin tsaro da muhimmanci fiye da yadda ake yi a yanzu.”
Kungiyar ta yabawa shugabannin NUT karkashin jagorancin Titus Audu Amba saboda abin da ta bayyana a matsayin mataki mai hikima da suka dauka domin jawo hankalin jama’a da gwamnati kan batun tsaron malamai da dalibai.