Aƙalla mutum 21 sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi a wani babban gini mai hawa a birnin Delhi na ƙasar Indiya.
Rahotanni sun ce marasa lafiya da ‘yan uwansu da ke karɓar kulawa a wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa ne ke zaune a ginin lokacin da gobarar ta tashi.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa ‘yan ƙasashen waje ne, ciki har da Najeriya, Mozambique, Bangladesh da Laberiya, waɗanda suka je Indiya domin neman lafiya ko kuma raka ‘yan uwansu marasa lafiya.
Shaidu sun ce wutar ta bazu cikin sauri, abin da ya sa mutanen da ke saman ginin suka kasa samun hanyar tsira cikin lokaci.
Wakilin BBC ya ruwaito cewa ‘yan sanda sun ce an shawo kan gobarar, sai dai har yanzu ba a tabbatar da musabbabin tashinta ba.