Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana kiwon shanu barkatai a cikin birnin Abuja a matsayin batu da ya shafi tsaron ƙasa, yana mai cewa matsalar na buƙatar tattaunawa ta gaskiya da kuma samar da mafita mai ɗorewa.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai-tsaye da manema labarai a ranar Litinin, inda ya nuna damuwa kan yadda ake ganin shanu suna kiwo a gefen tituna da kuma sabbin wuraren da aka bunƙasa a babban birnin ƙasar.
“Wannan batun tsaron ƙasa ne. Dole ne mu fuskanci gaskiya,” in ji ministan, yana mai cewa yunkurin magance matsalar kan fuskanci suka daga wasu da ke danganta lamarin da addini ko ƙabila.
Ya ce gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar matakan magance matsalar ta hanyar ƙarfafa tsarin kiwon shanu a ruga domin cire dabbobin daga cikin birane.
A cewarsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin aiwatar da tsarin ware wuraren kiwo domin rage yawo da shanu a cikin Abuja da sauran manyan birane.
Wike ya bayyana cewa ganin shanu suna yawo a cikin birni ba abu ne da ya dace da matsayin babban birnin ƙasa ba, yana mai kwatanta hakan da yadda ake gudanar da harkokin kiwo a wasu ƙasashe.
Ministan ya kuma yaba wa Ma’aikatar Bunƙasa Harkokin Kiwo da kuma ƙungiyar Miyetti Allah bisa tattaunawar da suke yi da masu ruwa da tsaki domin nemo mafita ga matsalar.
Sai dai ya amince cewa har yanzu ana ci gaba da fuskantar ƙalubalen, yana mai kira ga jama’a da su ba gwamnati haɗin kai wajen magance matsalar.
A wani ɓangaren kuma, Wike ya kare matakin gwamnatin FCT na korar masu kasuwanci daga manyan mahadar tituna da wuraren da ba a ware domin kasuwanci ba.
Ya ce gwamnati ta samar da kasuwanni da wuraren da suka dace domin gudanar da harkokin kasuwanci, yana mai jaddada cewa kasuwanci a gefen tituna na haifar da cunkoso da rashin tsari a cikin birni.
Ministan ya ce kiyaye tsafta, tsari da martabar Abuja na buƙatar haɗin kan gwamnati da al’umma, yana mai jaddada cewa ba za a amince da karya dokoki da sunan neman abin dogaro da kai ba.