Annaboar cutar kwalara ta yi ajalin sama da mutum 40, inda fiye da mutane 3,000 a ƙauyuka da unguwanni 139 da ke ƙananan hukumomi bakwai na jihar Borno ke fama da cutar cikin watan Mayun 2026.
A cewar rahotonni, annobar ta bazu a ƙananan hukumomin Maiduguri, Jere, Mafa, Konduga, Monguno, Ngala da Magumeri tsakanin ranar 1 zuwa 28 ga watan Mayu.
Bayanan da gwamnati ta bayar sun nuna cewa adadin mutanen da ta yi ajalinsu ya ƙaru daga 27 zuwa sama da 40 cikin kwanaki kaɗan, yayin da adadin masu ɗauke da cutar ya zarce 3,000.
Sai dai wasu iyalan marasa lafiya sun ce adadin na iya kasancewa ya fi haka saboda akwai waɗanda take halakasu a gidajensu ba tare da sunje asibiti ba.