Babban Mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga shugaba Tinubu, AbdulAziz AbdulAziz, yayi karin haske kan ɗaukar dakarun tsaron gandun-daji 1,000 a jihar Oyo.

 

A shafinsa na Facebook, AbdulAziz ya wallafa cewa jaridu sun fara ba da labarin aniyar ɗaukar masu tsaron daji (Forest Guards) guda 1,000 a jihar Oyo sakamakon satar mutane da aka yi kwanaki.

 

Ya yi la’akarin cewa wasu ƴan Arewa a kafafen sada zumunta na ƙorafi, ko shaguɓen cewa “an taɓa ƴan gata”. A ganin su, wannan abu ne kawai da ake yi domin Yarabawa saboda matsalar tsaro ta shafe su. To ba haka ba ne”, Inji shi.

 

Ya ƙara da cewa yanzu haka akwai jihohi 10 da aka kafa rundunar ‘Forest Guards’, kuma jihohin duk a Arewa suke. Ya ce kuma kowace jiha an ɗaukar mata mutum kimanin 1,000 ne.

 

Ya lissafto jihohin da ya ce tuni suna da dakarun tsaron gandun-dajin da suka haɗa da Borno, Yobe, Adamawa, Kwara, Sakkwato, Kebbi, Neja, Filato da Binuwai.

 

Ya ƙara da cewa akwai kuma waɗanda yanzu haka shirin kafa dakarun ya yi nisa, da suka haɗa da Kaduna, Edo, Kogi da Bauchi.