Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasarnan, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya nuna shakku kan ikirarin cewa jami’an tsaron kasarnan ba sa iya gano inda ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane suke, duk da cewa suna yawan wallafa bidiyoyi tare da sadarwa daga maboyarsu.


Buratai ya jaddada cewa hukumomin tsaro suna da ƙarfin gano irin waɗannan masu laifi.


Buratai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na TVC a ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan damuwar da ake nunawa game da yadda ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke amfani da kafafen sada zumunta da bidiyo wajen yaɗa ayyukansu a sassan ƙasar nan.


Janar ɗin mai ritaya ya ce bai yarda cewa jami’an tsaro ba su da karfin gano ‘yan bindigar da ke yawan bayyana ayyukansu a bainar jama’a ba.


Ya ce, “Ban gamsu cewa sun gaza gano su ba. Idan suna iya gano talakawan ƙasa ko masu tasiri a kafafen sada zumunta, ban ga dalilin da zai sa ba za su iya gano waɗannan ‘yan bindigar da ke nuna ganimarsu ko duk wasu ayyukan da suke yi a kafafen zamani ba.”


Duk da cewa bai yi suka kai tsaye ga jami’an tsaro ba, Buratai ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar wasu dalilai da ke tasiri kan yadda suke gudanar da ayyukansu.


Tsohon shugaban rundunar sojin ƙasar ya kuma jaddada buƙatar ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya ta hanyar ci gaba da horas da jami’an tsaro da ɗaukar ƙarin ma’aikata, da kuma inganta jin daɗin rayuwar jami’an tsaro.