Manoman garin Harbo Tsohuwa da kewaye a Jihar Jigawa sun gabatar da manyan korafe-korafe guda hudu kan Fulani makiyaya a wani taron fahimtar juna da aka gudanar tsakanin bangarorin biyu.


Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Sarkin Harbo Tsohuwa, Alhaji Ahmad Tijjani Akeel ya fitar bayan taron.


Sanarwar ta bayyana cewa an shirya taron ne domin tattauna matsalolin da suka taso tsakanin manoma da makiyaya da kuma nemo hanyoyin zaman lafiya a yankin.


A cewar sanarwar, manoman sun gabatar da manyan korafe-korafe 4 da suka hada da zargin Fulanin da lalata amfanin gona da gangan ta hanyar sassara ƴaƴan Kankana tun kafin su nuna.


Sai kuma lalata rijiyoyin noma ta hanyar cusa karare, itace da ƙasa a cikin fayif-fayif duk da cewar su ma fulanin na amfana da ruwan rijiyoyin.


Sai kuma zargin ƙwace, fashi da sace-sace a gida da gonaki.


Korafi na 4 shi ne na mutanen ʼYankunama waɗanda suka yi ƙorafin fulanin sun lalata musu gonakin rake.


Sanarwar ta kara da cewa bayan sauraron bangarorin biyu, shugabannin fulani makiyayan sun ce sun gamsu ba mamaki wasu daga cikin yaransu za su iya aikata irin wadannan aika-aika da ake zargi.


A ƙarshe zaman ya amince da ci gaba da tuntubar masu unguwanni a duk lokacin da wata matsala ta taso domin warware ta cikin lumana da fahimtar juna.