Majalisar Wakilan Nijeriya ta koma zaman majalisa bayan hutun makonni hudu da ta yi, inda aka samu sauya sheƙar wasu mambobin ta 13 zuwa wasu jam'iyyun.


Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, ne ya karanta takardun sauya sheƙar a zauren majalisar, lamarin da ke nuna ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027.


Daga cikin waɗanda suka sauya jam'iyya akwai Gaza Jonathan daga jihar Nasarawa, wanda ya fice daga SDP zuwa Labour Party, da Alex Egbona daga Cross River, wanda ya bar APC zuwa PDP.


Haka kuma Esosa Iyawe daga Edo, ya sauya daga APC zuwa NDC, yayin da Sani Lawal da Shehu Dalhatu daga Katsina suka fice daga APC, inda Dalhatu ya koma PDP.


A jihar Oyo kuwa, mambobi shida da suka hada da Adebayo Adepoju, Adedeji Olajide, Ojo Akinola, Oyedeji Oyeshina, Oyekunle Folajimi da Abass Adigun sun bar PDP tare da komawa APM.