Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yabawa Rundunar Sojin Ruwan ƙasar wacce aka ayyana a matsayin ta ɗaya a Afrika, bayan da aka kwashe tsawon shekaru 5 ba tare da anyi fashi a Tekun ƙasar ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin bikin da ake bikin cika shekaru 70 da kafuwar rundunar, wanda ya gudana a Eko Atlantic, da ke jihar Lagos.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin ruwan Najeriya ta samu ƙarin tagomashi a ayyukanta na samar da tsaro a kan tekun ƙasar, bayan da ta samu ƙarin wasu sabbin jiragen ruwa na yaƙi uku tare kuma da ƙaddamar da rundunar hadin gwiwa ta ruwa, da nufin tunkarar barazanar da ke kunno kai a mashigin tekun Guinea.
Commodore MS Shettima, babban kwamandan dakarun haɗin gwiwar ƙasashen 6, ya yi RFI Hausa ƙarin bayani.