Shugaban WHO Ya Ziyarci Yankin da Ebola Ta Fi Kamari a DRC

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya kai ziyara gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC), yayin da barkewar cutar Ebola ke ci gaba da yaɗuwa a yankin.

Da yake magana a Bunia, babban birnin lardin Ituri, Tedros ya ce al’ummar duniya na tallafa wa gwamnatin DRC wajen yaƙi da cutar, amma ya jaddada muhimmancin haɗin kan al’umma wajen dakile yaɗuwar ta.

Tun bayan ayyana barkewar Ebola a ranar 15 ga Mayu, an samu sama da mutum 1,000 da ake zargin sun kamu da cutar a DRC, yayin da mutane 246 suka rasu, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC).

WHO ta yi gargaɗin cewa adadin masu kamuwa da cutar na iya fiye da abin da aka ruwaito, saboda alamun sun nuna cutar ta fara yaɗuwa kafin hukumomi su gano barkewar ta.

A makwabciyar Uganda kuwa, an tabbatar da mutum tara sun kamu da Ebola, ciki har da mutum ɗaya da ya mutu, lamarin da ya sa ƙasar ta rufe wasu kan iyakokinta da DRC tare da tsaurara matakan killace matafiya.

Barkewar cutar na zuwa ne a daidai lokacin da yankunan gabashin DRC ke fama da rikice-rikice da rashin tsaro, abin da ke hana kai agajin lafiya da gudanar da gwaje-gwaje yadda ya kamata.

Kungiyar Doctors Without Borders (MSF) ta ce wannan barkewar ta Ebola ta nuna mafi yawan wadanda suka kamu da cutar a kwanaki biyar na farko idan aka kwatanta da sauran barkewar da aka samu a baya.

Ebola cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar hulɗa da ruwan jikin wanda ya kamu, kuma ta kashe fiye da mutane 15,000 a Afirka cikin shekaru 50 da suka gabata.