Shugaban Benin Ya Kai Ziyarar Aiki Ta Farko Nijar Domin Farfaɗo da Dangantaka
Sabon shugaban Jamhuriyar Benin, Romuald Wadagni, zai kai ziyarar aiki ta farko a Jamhuriyar Nijar yau Talata, inda ake sa ran zai gana da shugaban gwamnatin sojin ƙasar, Janar Abdourahamane Tiani.
Ana sa ran ganawar za ta mayar da hankali kan inganta dangantakar ƙasashen biyu bayan ta yi tsami a cikin ƴan shekarun nan, tare da tattauna batutuwan sake buɗe iyakoki, haɗin gwiwar tsaro da kuma maido da cikakkiyar hulɗar diflomasiyya.

Daga cikin manyan batutuwan da ake sa ran za su mamaye tattaunawar akwai aikin bututun ɗanyen mai mai tsawon kilomita 1,980 da ya haɗa filayen mai na Agadem da ke Nijar zuwa tashar jiragen ruwa ta Seme a Benin, wanda ake ganin yana da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasashen biyu.
Masu sa ido kan harkokin yankin na kuma fatan shugabannin za su tattauna yadda za a warware sabanin da ke tsakanin ƙasashen biyu kan zargin kasancewar dakarun musamman na Faransa a ƙasar Benin, batun da ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka janyo rashin jituwar bangarorin.
Kafin tafiyarsa zuwa Nijar, Wadagni ya gana da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a birnin Lagos ranar Litinin.
Rahotanni sun kuma nuna cewa shugaban na Benin zai wuce Jamhuriyar Burkina Faso bayan kammala ziyararsa a Nijar domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin ƙasashen yankin.