Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matsalar tsananin yanayin zafi da muhimmanci, yana mai danganta lamarin da sauyin yanayi da ke ƙara ta'azzara a faɗin duniya.
Guterres ya bayyana haka ne bayan Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya (WMO) ta yi gargaɗin cewa akwai buƙatar a fara shirye-shiryen fuskantar tasirin matsanancin zafin da ake sa ran zai ƙaru a watanni masu zuwa.
A cewar masana, wannan yanayi na iya haddasa ƙarin ɗumamar yanayi a yankuna da dama na duniya, tare da ƙara yawan matsalolin da ke da alaƙa da sauyin yanayi.
Masana sun ce irin wannan yanayi kan faru ne duk bayan shekaru biyu zuwa bakwai, kuma na baya-bayan nan ya taimaka wajen sa shekarar 2024 ta zama mafi zafi da aka taɓa samu a tarihi.