Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya sanar da sabuwar majalisar ministocin ƙasar, wadda ta haɗa da wasu jiga-jigan da suka yi aiki a ƙarƙashin jagorancin tsohon firaminista kuma aminin shugaban, Ousmane Sonko.
Sanarwar na zuwa ne kwanaki goma bayan korar Sonko daga muƙaminsa na firaminista, bayan watanni na saɓanin siyasa tsakanin shugabannin biyu.
Kafin korar tasa, Sonko ya riƙa sukar wasu matakan da gwamnatin Faye ke ɗauka domin tinkarar matsalar bashin da Senegal ke fuskanta.
Duk da cewa Sonko ya sha alwashin cewa jam’iyyarsa ta Pastef ba za ta shiga sabuwar gwamnati ba, sabuwar majalisar ministocin ta ƙunshi wasu mambobin jam’iyyar da suka yi aiki tare da shi a baya.
Jam’iyyar Pastef dai na da rinjaye a majalisar dokokin Senegal, kuma bayan korarsa daga muƙamin firaminista, ‘yan majalisar sun naɗa Sonko a matsayin kakakin majalisar dokokin ƙasar.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin sabon muƙamin zai ba Sonko damar ci gaba da taka muhimmiyar rawa a siyasar Senegal tare da ƙalubalantar manufofin gwamnatin Faye.