Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kuɓutar da fasinjoji 23 da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka sace a kan hanyar Ayegunle zuwa Bunu, a ƙaramar hukumar Kabba-Bunu ta jihar Kogi.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin X, rundunar ta bayyana cewa ta kai ɗauki ne bayan samun kiran gaggawa da sanyin safiya, lamarin da ya sa aka tura sojoji cikin gaggawa zuwa yankin.
Sanarwar ta ce maharan sun tare babbar hanyar tare da garkuwa da matafiya da dama kafin jami’an tsaro su isa wajen, sai dai sun tsere kafin isowar sojojin.
Duk da hakan, rundunar ta ce sojojin sun ci gaba da farmaki a hanyoyin da ake zargin maharan na bi, lamarin da ya haifar da gano motocin bas da kuma motar dakon kaya da aka watsar a kan hanya.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa mutum biyu sun rasu yayin harin, yayin da wasu biyar suka jikkata. An garzaya da su asibitin St. Joseph da ke Kabba, inda ake ci gaba da ba su kulawa.
Sojojin sun ce ana ci gaba da bincike domin gano tare da cafke waɗanda ke da hannu a harin.