Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bayyana cewa yankuna 178 da ke cikin kananan hukumomi 28 na Jihar Kano na cikin hadarin fuskantar ambaliya a bana.


Darakta Janar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta bayyana hakan yayin taron wayar da kan masu ruwa da tsaki da kaddamar da Shirin Shirye-shiryen Tunkarar Ambaliya na Kasa na shekarar 2026 a Kano. Ta ce hasashen da Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) da Hukumar Kula da Harkokin Ruwa (NIHSA) suka yi ya nuna cewa wasu yankunan Kano na iya fuskantar ambaliya.


Ta bayyana cewa NEMA ta gano kananan hukumomi 28 da ke cikin matsakaicin hadarin ambaliya, tare da yankuna 178 da ke bukatar daukar matakan kariya na musamman.


Ta kuma bukaci mazauna yankunan da ke cikin hadari su kasance cikin shiri tare da bin umarnin kwashe jama’a idan bukatar hakan ta taso.


A nasa jawabin, Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta amince da matakan rage ambaliya da suka hada da share magudanan ruwa, rushe gine-ginen da suka toshe hanyoyin ruwa da kuma shuka bishiyoyi miliyan 10.


Masu jawabi a taron sun jaddada muhimmancin yada bayanan gargadin yanayi ga al’umma domin rage asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon ambaliya.