An harbe mutane biyu a garin Nanyuki da ke tsakiyar Kenya yayin da ake ci gaba da zanga-zanga kan shirin Amurka na kafa cibiyar killace masu Ebola a wani sansanin soji da ke yankin.
Rahotanni sun ce an harbi ɗaya daga cikin mutanen a kusa da sansanin sojin sama da ke Laikipia, inda ake gudanar da zanga-zangar, kuma ya rasu bayan da aka garzaya da shi asibiti. An kuma kai gawar mutum na biyu asibiti ta hannun sojoji.
A halin yanzu ba a bayyana musabbabin mutuwar mutanen ba, kuma hukumomi ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Zanga-zangar dai ta ɓarke ne a ranar Litinin, inda ɗaruruwan mutane suka fito kan tituna, suka tare hanya tare da ƙona tayoyi, yayin da ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa su.
Masu zanga-zangar na nuna adawa da shirin Amurka na kafa cibiyar kula da masu Ebola a Kenya, suna fargabar yiwuwar bazuwar cutar a ƙasar.
A cewar rahotanni, cibiyar mai gadaje 50 za ta kasance ƙarƙashin kulawar likitocin Amurka, kuma za a yi amfani da ita wajen kula da Amurkawa da suka kamu da Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Zuwa yanzu dai babu rahoton ɓarkewar cutar Ebola a Kenya.