Gwamnatin Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan rashin kuɓutar da ɗaliban makaranta 42 da aka sace a jihar Borno, waɗanda har yanzu ke hannun ƴan bindiga.
Iyayen ɗaliban sun bayyana damuwa da cewa gwamnati kamar ta yi watsi da lamarin, inda suka kwatanta yadda ake ganin ana ɗaukar matakan gaggawa a wasu jihohi kamar Oyo, yayin da nasu batun ke tafiyar hawainiya.
Sai dai mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz, ya musanta zargin, yana mai cewa gwamnati na ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin ganin an kuɓutar da yaran.
Rahotanni sun nuna cewa ɗaliban sun shafe kwanaki 17 a hannun masu garkuwa tun bayan sace su a garin Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira Uba.
Wani shugaban al’umma a yankin, Dakta Chi Namke, ya shaida cewa iyaye na cikin tashin hankali saboda yaran da aka sace ƙanana ne, tare da koka da ƙarancin ziyartar yankin daga hukumomin tarayya.
Shi ma shugaban gamayyar ƙungiyoyin farar hula a Arewa maso Gabas, Ambasada Ahmad Shehu, ya buƙaci gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki, yana mai cewa haƙƙin gwamnati ne ceto ɗaliban cikin gaggawa.
A gefe guda, gwamnatin tarayya ta ce zargin iyayen ɗaliban na da nasaba da siyasa, tana mai jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙari wajen ganin an warware lamarin.
A yau Talata kuma, ƙungiyar ƙwadago ta malaman makaranta (NUT) na shirin jagorantar zanga-zanga a sassan ƙasar domin matsa lamba ga gwamnati ta gaggauta ceto ɗaliban.