malamai a sassa daban-daban na Najeriya sun fito zanga-zanga a faɗin ƙasar, inda suke neman a gaggauta kuɓutar da ɗaliban da aka sace a jihohin Oyo da Borno.
Zanga-zangar, wadda ƙungiyar malaman Najeriya (NUT) ta shirya, ta soma ne a ranar Litinin, inda jihohi da dama suka shiga ciki har da Borno, Kano, Legas, Akwa Ibom da Abuja, tare da bin sahun Oyo da Ogun da suka fara gudanar da ita tun farko.
Ƙungiyar ta ce matakin nuna goyon baya ne ga takwarorinsu da kuma ɗaliban da ke hannun masu garkuwa, bayan jerin hare-hare kan makarantu da suka haifar da fargaba a tsakanin iyaye da malamai.
A biranen Maiduguri, Uyo da Legas, malamai ɗaruruwan sun yi tattaki kan tituna suna rera waƙoƙi tare da ɗaga alluna, inda suka buƙaci a gaggauta sakin ɗalibai da malamai da aka sace.
Masu zanga-zangar sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro a makarantu da kuma yankunan ƙasar baki ɗaya domin dakile matsalar satar mutane da ke ƙara ta’azzara.