Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da Olaide Busayo Adegoke John-Paul, ƙanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki na Najeriya kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Oyo a jam’iyyar APC, Adebayo Adelabu, tare da ’ya’yanta tagwaye biyu.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba a unguwar Challenge da ke birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Wani mai taimaka wa Adelabu kan harkokin yaɗa labarai, Femi Awogboro, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa wasu mahara ɗauke da makamai ne suka tare su yayin da suke cikin tafiya a cikin birnin.
A cewarsa, an yi garkuwa da Misis Olaide Busayo Adegoke John-Paul mai shekaru 43 da misalin ƙarfe 7:30 na safe yayin da take kan hanyarta ta kai yaranta makaranta a Ibadan.
Ya ce maharan sun kuma tafi da yayanta tagwaye masu shekaru 12, Peter da Paul, waɗanda ke tare da ita a lokacin da aka kai harin.
Awogboro ya bayyana cewa Misis Olaide ita ce auta cikin yaya biyar na Misis Olufunmilayo Aduke Adegoke Adelabu.