Iska mai ƙarfi ta lalata gidaje da muhimman gine-ginen jama’a a garuruwa tara da ke Karamar Hukumar Augie ta Jihar Kebbi.
wannan na cikin sanarwar da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, ta fitar.
Sanarwar ta ce garuruwan da abin ya shafa sun hada da Gidan Agoda, Fadisonku, Saharma, Tunga Mai Ruwa, Yalema, Tiggi, Gadawande, Lugga da Gidan Mai Gatari.
NEMA ta bayyana cewa iskar ta lalata gidaje, asibitoci, masallatai da makarantu, inda rufin gidaje da dama ya yaye yayin da wasu gine-gine suka rushe, lamarin da ya jefa wasu mazauna yankin cikin mawuyacin hali.
Hukumar ta ce za ta mika sakamakon bayanan tantancewar da ta yi ga hukumomin da suka dace domin duba yiwuwar kai agajin jin kai ga wadanda bala’in ya shafa, tare da kira ga al’umma su rungumi matakan kare muhalli da dashen itatuwa domin rage illar irin wadannan bala’o’i.