Hukumomin tsaron gaɓar teku na ƙasar Mauritania sun ceto baƙin haure 110, ciki har da mata 12 da yara uku, bayan jirgin ruwansu ya samu matsala a tsakiyar teku yayin da suke ƙoƙarin isa Turai.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce baƙin hauren sun taso ne daga birnin Banjul na ƙasar Gambia da nufin ƙetare Tekun Atlantika zuwa Turai.
Daga cikin mutanen da aka ceto akwai ’yan ƙasar Mali 80, ’yan Senegal 12, ’yan Gambia 10, ’yan Mauritania huɗu, ’yan Ivory Coast uku da kuma ɗan ƙasar Najeriya guda ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa shekaru da dama kenan dubban matasa daga ƙasashen Afirka ta Yamma ke yunƙurin isa Turai ta hanyar ƙetare Tekun Atlantika, duk da haɗarin da ke tattare da wannan tafiya.