Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara bincike kan zargin fallasa bayanan jarumi Emeka Ike, daga rumbun bayanan rajistar masu kaɗa ƙuri’a, tare da zargin amfani da damar shiga shafin hukumar ba bisa ƙa’ida ba.


Lamarin ya samo asali ne bayan Emeka Ike ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan mai taimaka wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, wato Lere Olayinka, bisa zargin kutse da fallasa bayanansa daga shafin INEC ba tare da izininsa ba.


Kwamishinan INEC kuma shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Kaɗa Ƙuri’a, Mohammed Haruna, ya ce binciken ya biyo bayan zargin shiga bayanan tsarin Rajistar Masu Kaɗa Ƙuri’a (CVR) ba tare da izini ba da kuma wallafa bayanan Emeka Ike, wanda ya tsaya takara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar NDC a Abuja.


INEC ta bayyana lamarin a matsayin mai matuƙar muhimmanci, inda ta ce ta fara cikakken bincike domin gano yadda aka samu damar shiga bayanan.