Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da sace ɗalibai da malamansu a Jihar Oyo, inda ya bayyana lamarin a matsayin wata alama da ke nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Phrank Shaibu, ya fitar yau Laraba, Atiku ya ce garkuwa da mutanen ya sake bayyana gazawar gwamnati wajen magance matsalar rashin tsaro yadda ya kamata.
Atiku ya kuma soki rahotannin da ke cewa an tura wasu jami'ai zuwa ga iyalan waɗanda abin ya shafa domin kai musu kayan tallafi, yana mai cewa irin waɗannan matakan ba za su magance damuwar da iyayen ke ciki wanda har yanzu 'ya'yansu ke hannun masu garkuwa da mutane ba.