Aƙalla mutum 63 ne suka jikkata sakamakon harin da Iran ta kai kan Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Kuwait, kamar yadda Ma’aikatar Lafiyar ƙasar ta sanar.

Daga cikin waɗanda suka jikkata akwai ma’aikatan filin jirgin sama da fasinjoji, yayin da rahotanni suka nuna cewa harin ya haddasa lalacewa mai yawa a ginin Terminal 1 da kuma wasu wuraren jakadanci.

Tun da farko, Ma’aikatar Harkokin Wajen Kuwait ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a harin.

Iran ta bayyana cewa ta kai harin ne saboda zargin da take yi cewa Amurka na amfani da ƙasar Kuwait wajen kai hare-hare a kanta, tare da ɗora alhakin lamarin kan shugabannin Kuwait.

A martaninsu, Kuwait da Qatar sun yi Allah wadai da harin, suna masu bayyana shi a matsayin matakin da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.