Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin hannu a harin da aka kai Cocin Katolika ta Saint Francis da ke Owo a Jihar Ondo a ranar 5 ga Yunin 2022.
Mai Shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin ne bayan kotun ta same su da laifuka tara da suka haɗa da ta’addanci, haɗa baki domin aikata laifi, satar mutane da kuma kashe masu ibada sama da 40 a harin da ya girgiza Najeriya.
Waɗanda aka yanke wa hukuncin na daga cikin mutum biyar da Hukumar Tsaro ta DSS ta gurfanar kan zargin hannu a harin, wanda ya kuma yi sanadin jikkatar fiye da mutum 100.
Kotun ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa mutanen huɗun ba tare da wata shakka ba, lamarin da ya sa aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Sai dai kotun ta wanke mutum na biyar daga cikin waɗanda ake tuhuma, bayan da ta ce ba a gabatar da isassun hujjojin da za su tabbatar da laifinsa ba.
Harin da aka kai Cocin Saint Francis a Owo ya jawo allawadai daga sassa daban-daban na Najeriya, tare da ƙara nuna damuwa kan matsalar tsaro da hare-haren ta’addanci a ƙasar.