Majalisar Dokokin Najeriya Ta Yi Kira da A Gaggauta Kuɓutar da Ɗalibai da Malamai da Aka Sace a Oyo da Borno
Majalisar Dokokin Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya tare da hukumomin tsaro da su gaggauta aikin kuɓutar da ɗalibai da malamansu da aka sace a jihohin Oyo da Borno.
Wannan kiran na zuwa ne a daidai lokacin da damuwa ke ƙara ƙamari kan yawaitar satar ɗalibai a sassa daban-daban na ƙasar.
Majalisar Wakilai ta bayyana cewa matsalar na ƙara zama babbar barazana ga harkar ilimi da rayuwar yara, yayin da Majalisar Dattawa ta jaddada bukatar ƙara tsaurara matakan tsaro a makarantu domin hana sake aukuwar irin wannan lamari.
A halin da ake ciki, Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) ta gudanar da zanga-zanga a wasu jihohi, inda take matsa lamba ga gwamnati da ta gaggauta ceto ɗaliban da ke hannun masu garkuwa.
Sanata Ali Ndume, a wata hira da BBC, ya ce halin da ake ciki na matuƙar tayar da hankali musamman ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
Ya bayyana cewa ya tattauna da wasu ‘yan majalisa, kuma an gabatar da ƙuduri a Majalisar Wakilai kan yaran da aka sace a Borno tun ranar 15 ga watan Yuni.
Ya ce har yanzu akwai kusan mutane 416 da ke hannun ‘yan bindiga da aka sace daga Gwashe, ciki har da ƙananan yara masu shekaru biyu zuwa uku.
Ndume ya kuma yi gargaɗi cewa satar mutane na ƙara zama kamar hanyar samun kuɗi ga masu aikata laifin, sakamakon rashin tsauraran matakan da ake ɗauka.
Ya buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa da ƙarfi domin dakile matsalar, yana mai cewa idan aka jajirce za a iya shawo kanta.