Wata sanarwa kan ayyukan dakarun Najeriya da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya samu a ranar Laraba ta bayyana cewa sojojin sun samu gagarumar nasara bayan ƙaddamar da jerin hare-hare a jihar Borno.
Sanarwar ta ce rundunar ta kai farmaki a yankunan Kirta da Arina Cika, inda aka kashe kwamandojin ƴan ta’adda da dama, ciki har da wani mai suna Khalifa Umar, wanda aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan mayaƙan ISWAP.
Ta ƙara da cewa hare-haren sama da dakarun suka kai sun tilasta wa ƴan ta’addan da suka tsira barin mafakarsu da ke cikin tsibiri, inda suka koma kan tudu domin gujewa farmakin sojoji.
Haka kuma, a wani samame daban, dakarun sun kama wasu da ake zargi da taimaka wa ƴan ta’adda ta hanyar samar musu da ababen hawa da kuma bayanan sirri. Rahoton ya kuma nuna cewa an kama wani tsohon soja da ya yi ƙauracewa aiki, wanda daga bisani aka gano yana da hannu a wasu laifuka.
A wani ɓangare na farmakin, dakarun sun kai hari a yankin Kukawa, inda suka fatattaki ƴan ta’adda tare da gano wasu makamai da suke amfani da su wajen kai hare-hare a Borno da yankunan da ke kewaye.