Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana Ta Samar da Guraben Aiki 120 Ga Waɗanda Aka Maido Daga Afirka Ta Kudu
Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ta samar da guraben ayyukan yi guda 120 ga ‘yan ƙasar da aka dawo da su daga Afirka Ta Kudu, biyo bayan tashin rikicin ƙin jinin baƙi da ya addabi ƙasar.
A cewar ma’aikatar, an samar da ayyukan ne ta hanyar haɗin gwiwa da ‘yan kasuwa a ƙasar, a wani yunƙuri na tallafa wa mutanen da suka baro dukiyoyinsu da sana’o’insu a Afirka Ta Kudu domin tsira da rayukansu.
Ministan harkokin wajen Ghana ya yi kira ga ‘yan kasuwa da masu kamfanoni masu zaman kansu da su ba wa irin waɗannan mutanen damar aiki domin sake dawo da rayuwarsu kan turba.
Ayyukan na ƙarƙashin ofishin da ke kula da maido da ‘yan ƙasar daga ƙetare, wanda ke ƙarƙashin jagorancin Alexander Grant Ntrakwa.
Zuwa yanzu, gwamnati ta ce ta riga ta mayar da mutane kusan 300 gida daga Afirka Ta Kudu a wani mataki na kare su daga rikicin ƙin jinin baƙi da ke ci gaba da faruwa.
Gwamnatin Ghana ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da maido da dukkan ‘yan ƙasarta da ke son komawa gida, tare da bayyana shirin ɗaukar matakan diflomasiyya kan lamarin.